Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Taimakawa 'Yan Gudun Hijira Inji Amina Dogarai


Amina Dogarai

A shirinmu na mata a yau mun zanta da jami’ar walwala ta Gidauniyar Kwandala foundation inda a shekarar da muka yi ban kwana da ita ne suka taimaka wa 'yan gudun hijira.

Malama Amina Dogarai ta ce gidauniyarsu na taimakawa masu karamin karfi mussaman ma mata da kananan yara, wani lokacin ma har da marasa karfi

Ta ce a duk karshen shekara su kan kai taimakonsu wurare daban daban inda a wannan shekarar suka je gidajen masu rangwamen hankali na Dawanau da 'yan gudun hijira mussaman ma marayun da gwamnatin Kano ta yi wa gida a Kano

Daga cikin kayayyakin da suke bayar wa sun hada da kayan abinci , da kayan sawa da kayayyakin masarufi

Idan kuwa matsalar ta rashin lafiya ce sukan kai marasa lafiya asibitoci domin a duba lafiyarsu

Ta bukaci jama'a masu hannu da shuni da taimakawa masu gudun hijira.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG