Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahaifinta Ya Mara Mata Baya


A shirinmu na mata a yau mun sami zantawa da wata matashiya Amina Ahmad Abdulkarim mai karantar Marketing wato ilimi kasuwanci.

Amina Ahmad ta ce ta zabi kwas din Marketing ne saboda ikirarin da ake yi na cewar kwas ne da Maza ne kadai ke yi, domin ta nunawa 'yan uwanta mata cewar babu wani kwas da namiji zai yi da mace ma ba zata iya ba , muddin tana da sha’awa da burin zamo wani abu a rayuwa.

Ta ce ta zabi kwas din ne duk kuwa da cewa a Nijeriya ba duk kwas din da mutum ya karanta zai sami gurbin aiki a wannan fanni ba, tana mai cewa mahaifinta ya maramata baya kan zaban kwas din.

Daga bisani ta umarci mata dasu tashi tsaye su nemi ilimi domin a cewarta shi zai taimaka masu a rayuwarsu ta yau da kullum.

Ku biyo domin jin tattaunawar mu da matashiya Amina Ahmad.

XS
SM
MD
LG