Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muna Duba Hanyoyin Kare Kananan Yara: In Ji Apple


Yayin da yake kare manufofinsa game da kananan yara, kamfani Apple ya ce a koda yaushe yana duba hanyoyin kare kananan yara, bayan da manyan masu zuba hannun jari biyu a kamfanin suka nemi kamfanin ya ‘dauki matakin shawo kan matsalar shakuwa da yara suke yi da wayar iPhone.

Masu hannun jari Jana Partners da CalSTRS sun aikawa da Apple wasika ranar Asabar suna neman kafanin ya kirkiri wata manhaja da zata baiwa iyaye damar kayyade amfani da wayoyin zamani.

Jiya litinin ne kuma Apple ya ce tun shekarar 2008 manhajar wayar iPhone ke baiwa iyaye damar kayyade abin da yayansu zasu iya yi a wayoyinsu.

A wata sanarwa da Apple ya fitar ta ce “Muna yin tunani mai zurfi kan yadda ake amfani da kayayyakinmu, da kuma irin yadda yake shafar masu amfani da fasaharmu a fadin duniya.” Ta ci gaba da cewa “muna daukar alhakin da ya rataya a wuyanmu da muhimmanci, mun kuma kuduri aniyya1r ganin cewa mun farantawa masu amfani da kayan mu.”

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:08 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG