Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mike Tyson Zai Yi Gonar Shukawa Da Sarrafa Wiwi


Mike Tyson
Mike Tyson

Tsohon zakaran damben duniya, Mike Tyson, yana shirin zamowa wani zakaran a masana'antar sarrafa ganyen Wiwi ta Jihar California dake kara bunkasa tun bayan da jihar ta halalta shan tabar wiwi a farkon wannan shekara.

Mike Tyson da wasu abokan huldar kasuwancinsa, sun aza harsashin gina gidan gona mai fadin eka 40, inda suke sa ran masu shukawa da masu amfani da ganyen na wiwi zasu rika kwarara duk rana.

Tun kafin ranar 1 ga watan Janairun nan ma, Jihar ta California ta kyale ana amfani da ganyen wiwi, amma wajen jinyar wasu cuce-cuce.

Jaridar The Blast ta ruwaito cewa tun a watan jiya Mike Tyson, mai shekaru 51 da haihuwa, ya aza harsashin ginin abinda aka bayyana da sunan "Gandun Shakatawa na Wiwi" a wani gari mai suna California City dake cikin hamadar Mojave, kimanin mil 110 a arewa da birnin Los Angeles.

Wannan wuri ba ya da nisa daga sansanin mayakan saman Amurka na Edwards.

Sunan kamfanin da ya kafa don gudanar da wannan aikin shine Tyson Holistic, yayin da za a rika kiran wannan gandu da sunan Tyson Ranch.

An ba da rahoton cewa gonar ta Tyson Ranch zata kebe fili mai fadin eka 20 domin "kwararrun manoman ganyen wiwi" yayin da za a gina wuraren da masu noma da wadanda ke son zamowa manomanta zasu hadu su yi cudanya.

A bayan haka kuma, za a kafa masana'antar sarrafa abubuwan ci da sha wadanda ake yi da ganyen wiwi, da gidan sinima, da wuraren shakatawa irin na tantuna da ake yi a waje.

An aza harsashin wannan aikin tare da wasu abokan huldar kasuwancin Mike Tyson biyu, watau Robert Hickman da Jay Strommen, har ma da magajiyar garin na California City, Jennifer Wood. Ta ce wannan gidan gona zai taimaka sosai wajen sake farfado da wannan gari nata, wanda ya kasa bunkasa kamar yadda wadanda suka tsara gina shi a shekarun 1950 suka yi tsammani tun da farko.

A can baya, Tyson ya sha cewa lallai yana shan tabar wiwi. A watan Oktoba na shelkarar 2000 ma, ya doke wani dan dambe mai suna Andrew Golota, amma daga baya sai aka canja wannan sakamako zuwa kunnen doki a bayan da aka gano cewa Tyson ya sha tabar Wiwi kafin damben.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG