Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Fashin Baki Kan Al'amuran Wasanni Sun Yi Tsokaci Kan Wasan Manchester City Da Arsenal


Kocin kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Pep Guardiola, ya ce kungiyarsa ta cancanci samun nasara a wasannin lig na bana ganin yadda ta doke kungiyar Arsenal, a wasa na farko ta gasar Firimiya lig 2018/19 ta Ingila.

Manchester City, ta doke ta da ci 2-0 dan wasan City Raheem Shaquille Sterling, shi ya jefa kwallon farko a minti na 14 da fara wasan daga bisani bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, Bernardo Silva, ya zurara kwallo ta biyu a ragar Arsenal a mintuna na 64.

Bayan haka kuma Manchester city, tafi Arsenal taka leda a wasan inda take da kashi 59 cikin dari na kokari a wasan, ita kuwa Arsenal duk da a gidanta ake wasan tana da kashi 41.

Wasu masu fashin baki kan al'amuran wasannin kwallon kafa na ganin saboda sabon Kocin da Arsenal, ta kawo wato Unai Emery, domin bai gama sanin kafar ‘yan wasan ba tukum, wasu kuma suna ganin Kocin bazai iya bane.

Kyaftin din Barcelona Lionel Messi, ya lashe Kofuna 33 tare da kulob din - inda ke gaba da Andres Iniesta, da guda daya.

Messi, ya samu wannan nasaranne a wasan karshe da suka doke Sevilla da ci 2-1 a ranar lahadi da ta gabata na Spanish Super Cup.

Shi kuwa takwararta Cristiano Ronaldo, ya zura kwallonsa ta farko a kungiyar Juventus, a wasan da suka yi da matasan kungiyar wato (Team B) na Juventus, cikin wasannin da aka saba yi duk shekara, anayin wasa a kowace shekara tun daga 1955.

Juventus B ta lashe wasan farko da ci 3-2 amma shine nasara ta farko tun a shekarar 2005.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:38 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG