Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Chelsea ta Kulla Yarjejeniya da Maitsaron Raga Kepa


Maitsaron raga na kungiyar Chelsea Thibaut Courtois ya sanya hannu kan yarjejeniyar kwantirakin shekaru shida tare da Real Madrid a ranar Alhamis, inda ya kammala zaman shekaru bakwai a Chelsea.

"Wannan shi ne mafi kyan kulob a duniya," in ji Courtois, wanda ya sanya hannu a Chelsea a Yuni 2011 daga kungiyar Genk.

Courtious ya zauna a Atletico Madrid, a matsayin aro daga Chelsea inda ya dawo kulob dinsa na Chelsea a 2014. Ranar Litinin da ta gabata Courtois bai halarci horar da 'yan wasa na Chelsea ba, wanda ana ganin yana da nasaba da shirin barin kungiyar, don hadewa da Real Madrid.

Ita Kungiyar Chelsea ta kulla yarjejeniya da maitsaron raga Kepa Arrizabalaga daga Athletic Bilbao a kan zunzurutun kudi har fan miliyan 71, hakan na nuni ya fi kowanne maitsaron raga tsada a duniyar kwallon kafa.

Kepa, mai shekaru 23, ya zo Stamford Bridge bayan da aka kammala yarjejeniya ta kwantirakinsa, ta sanya hannu a kwangilar shekaru bakwai a kulob din kuma ya maye gurbin Thibaut Courtois, wanda ya koma kungiyar Real Madrid.

Kepa shine zabin na biyu da Real Madrid taso saya bayan David de Gea na Manchester United. Ya shafe shekaru biyu a tawagar farko ta Athletic, inda ya buga wasanni 53 a La Liga, "Kepa yace abubuwa da yawa sun jawo hankalinna zuwa ga kulob din na Chelsea, kuma ina farin ciki da Chelsea ta yanke shawarar amincewa da ni kuma ta dauke ni."

A watan Janairu, Kepa ya sanya hannu a sabon kwangilar tare da Athletic Bilbao, har zuwa 2025, ba tare da sha'awar Real Madrid ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00

  • 16x9 Image

    Daula Saleem

    Daula Saleem, Ma’aikaciyar Jarida ce (International Broadcaster - Multimedia) a Sashen Hausa na Muryar Amurka dake birnin Washington, D.C. Yar asalin Jihar Katsina. Ta karanta aikin Jarida a Jami’ar Bayero University Kano.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG