Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manchester United Ta Ki Amincewa Da Tayin Barcelona Akan Paul Pogba


Ana alakanta shahararren dan wasan tsakiyar nan kwallon kafa wanda ya koma kungiyar Manchester United akan kudi Fam Miliyan 89, a shekarar 2016, da ficewa daga kungiyar a karshen kakar wasannin bana a sakamakon rashin tauba abun kirki da kungiyar ta yi.

Rahotanni daga kasar Spain sun bayyana cewa matashin dan wasan mai shekaru 25 da haihuwa na neman sauya sheka zuwa wata sabuwar kungiya yayin da dillalin dan wasan ya bukaci sayar da shi ga kungiyar Manchester City a cikin watan Janairu.

Mujallar the Guardian, ta wallafa cewa kungiyar Manchester United, ta ki amincewa da tayin da kungiyar Barcelona ta yi na kudi Fam Miliyan 50, akan dan wasan.

Kungiyar Manchester United bata son sayar da dan wasan musamman ma akan kusan rabin kudin da ta saye shi a shekaru biyu da suka gabata.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG