Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masoya Kwallon Kafa A Jamhuriyar Nijar Sun Kadu Da Samun Labari Rasuwar Stephen Keshi


A Jamhuriyar Nijer ma’abota wasannin kwallon kafa sun kadu sosai dangane da samun labarum rasuwar tsohon kocin kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles, Stephen Keshi.

Cewar kwac maye Jin Yabo “Stephen keshi mutum ne da ya rike matsayi daban daban a kungiyar kwallon kafa ta Najeriya kuma an sanshi da hazaka, kuma ya zamam kyaftin na kungiyar ‘yan wasan kusan lokaci daya da daya daga cikin manyan kwac din kasar Nijar, dan haka muna addu’a Allah ya jikan shi, ya yi masa rahama”.

Ya kara da cewa “mutum ne mai hakuri kumaya taba rike kungiyarvkwallon kafa ta Togo, ya dawo ya kuma rike Najeriya kuma yayi aiki da aminci”.

Daga karshe kwac din ya aika da sakon ta’aziyyar sag a dukkan dauakacin ‘yan wasan kwallon kafa na Najeriya da iyalai da ma dukkan ‘yan Najeriya bisa wannan babban rashi.

Ga cikakken rahoton.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG