Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ra'ayoyin Wasu 'Yan Niger Delta A kan Rasuwar Stephen Keshi Da Shu'aibu Amodu


A yayin da ake ci gaba da juyayin rashin da kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ta yi na Mr Stephen Keshi da Shu’aibu Amodu, jama’a daga yankin Niger Delta na ci gaba da tofa albarkacin bakin su inda wasu da dama suka bayyana cewa lamarin ya girgiza su kwarai, yayin da wasu kuma a tasu cewar akwai bukatar gwamnati ta tashi tsaye wajan bincikawa domin gano misabbabin rasuwar wadannan fitattun gwarzaye biyu a kusan lokaci guda.

Wasu da dama sun bayyana cewar irin hidimar da wadannan mutane suka yi wa kasar su Najeriya da kuma ‘yan Najeriya, sun can-can ci yabo da kuma girmamawa musamman duba ga irin rawar da suka taka a kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles.

Shi dai Stephen Keshi an haife shi ne a shekarar 1962 a garin Azare na jihar Bauchi, kuma ya yi fice wajan taka leda da kuma haras da ‘yan kwallo a nahiyar Afirka, shine mutum na biyu a nahiyar Afirka da ya dauki kofi a gasar cin kofin Afirka a matsayin sa na dan wasa.

Keshi dan wasan baya ne, kuma ya buga yawancin wasannin sa a kungiyoyin kasa da kasa kana daga bisani ya je kasar Amurka inda ya yi nazari akan dabarun horas da ‘yan wasa, kuma ya buga wasa a kungiyoyi 11 na tamaula a duniya.

Shi kuwa Shu’aibu Amodu ya rasu ne yana da shekaru 58 a duniya, kuma dan asalin jahar Edo ne dake yankin Niger Delta. Ya fara jagorantar kungiyar kwallon kafar Najeriya tun yana da shekaru 36 a duniya.

A shekarar 1994 marigayin ya smarwa da kungiyar Super Eagles gurbin shiga wasan cin kofin duniya, da shekarar 2002, da kuma shekarar 2010, sai dai bai jagoranci tawagar zuwa wasan ba, a lokacin sa ne kasar ta kare a mataki na uku a gasar cin kofin Afirka a Mali a shekarar 2002, da Angola a shekarar 2010.

Saurari cikakken Rahoton.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG