Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Magoya Baya Ingila Da Na Rasha Sun Baiwa Hammata Iska


A ci gaba da wasan Copa America, da ake yi ayi waje da Brazil, inda Peru, ta doke Brazil, sakamakon wasan ya nuna cewa Equado da Peru, sun samu nasarar zagaye na karshe.

Sai kuma wasan da aka buga tsakanin Amurka, da Paruguay, inda Amurka, ta samu nasara, ita kuwa Costa Rica, ta nakadawa Columbia kashi da ci uku da biyu.Wasan gobe za’a buga tsakanin Mexico da Venezuela, sai Uruguay da Jamaica.

A gasar nahiyar kasashen Turai kuma da aka fara ranar juma’a da ta gabata a yau za’a yi wasa tsakanin Spain da Czech Republic, Ireland da Sweden sai kuma Belgium da Italy.

Magoya bayan kungiyar kwallon kafar Ingila, da na Rasha, sun baiwa hammata iska, inda suka jiwa juna rauni. Hukumar kulla da wasan kwallon kafa na nahiyar Turai, ta gargadi kasashen biyu da su ja kunnen magoya bayan su domin idan irin haka ya sake faruwa to za’a dakatar dasu.

XS
SM
MD
LG