Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mawakin (Shegiyar Uwa) Yayi Mummunar Hatsari! Amm Yana Nan Da Rai


Haruna Ningi
Haruna Ningi

Shahararren mawakin nan mai suna Haruna Aliyu Ningi yayi mummunan hatsarin mota yau Asabar da rana a hanyar Bauchi zuwa Jos.

A wasu majiyoyi na kusa dashi da dama sun bayyana cewa ya samu buguwa ne kawai amma yana nan da ransa ba kamar rade radin da aka fara ji cewa ya rasu ba.

Shidai Haruna Aliyu Ningi ya shahara da wakoki irnsu (shegiyar uwa) da (ku fada wa Obasanjo bamu yarda ta zarce ba).

Wadanda suka ga hatsarin sun bayyana cewa ana kyautata zaton cewa tsananin gudu ne ya haddasa wannan hatsari

Yanzu haka dai likitoci sun ce ya sami buguwa a kirjinsa ne amma an sallame shi sai dai ance gobe idan Allah ya lkaimu zai sake komawa asibiti domin a duba kirjin nasa.

Mawakin yana cikin motar sa ne tare da kanwarsa da diyar ta da kuma wani abokin sa akan hanyar sa zuwa Jos.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG