Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manchester United Ta Yi Kacha Kacha Da Burton Albion


Paul Pogba
Paul Pogba

An fidda jaddawalin kungiyoyin da zasu kara a wasan zagaye na sha shida na gasar cin kofin English football league, na kasar Ingila.

Kafin a fitar da wannan jaddawalin sai da kungiyoyin kwallon kafa na kasar ingialar suka gwabza a tsakaninsu inda akayi waje rod da wasu,

A jiya laraba 20/9/2017 kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, ta doke Burton Albion da kwallaye 4 -0 Chelsea ta lallasa Nottingham Forest, daci 5-1, sai Everton 3-0, Sunderland, Westbromwich 1-2 Manchester City, Arsenal kuwa ta samu nasara da kwallo 1-0 tsakaninta da Doncaster Rivers.

Ga kuma jirin sunayen kungiyoyi sha shida da zasu kara a tsakaninsu a zagayen gaba. AFC Bournemouth da Middlesbrough's,Leicester City da Leeds United, Manchester City da Wolverhampton, Chelsea da Everton,

Sauran wasannin kuwa za'a gwabza ne tsakanin Arsenal da Norwich City, sai Swansea da Manchester United, Kungiyar kwallon kafa ta Bristol City da Crystal palace, Tottenham zasu karbi bakuncin Westham United.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG