Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manchester United Ta Yiwa Magoya Bayanta Kashedi


Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, tayi kira ga magoya bayanta da suguji a abinda zai zubda, mutuncin kungiyar a idon ‘yan wasan kwallon kafa da ma duniya, baki daya.

Manchester tayi wannan kiran ne sakamakon abinda ya faru a wasan da kungiyar tayi da takwararta ta Everton, a gasar cin kofin Firimiya lig na bana wasan mako na biyar a ranar lahadi 17/9/2017. inda Manchester United ta lallasa Everton daci 4-0.

Kungiyar tace magoya bayanta sun rera wakoki iri iri na nuna na nuna banbancin launin fata ga dan wasanta Romelu Lukaku, wanda ya jefa kwallo na uku a wasan.

Manchester United ta nuna bacin ranta ga magoya bayan ta kuma tace yin haka ya sabawa dokar hukumar kwallon kafa ta kasar Ingila (FA).

Kungiyar ta Manchester United tace wannan bashi ne karon farko da akaji magoya bayanta suna irin wannan wake wake nuna banbancin launin fata ba, domin sunyi haka a wasan da kungiyar ta Manchester, tayi da Basel, na gasar cin kofin zakarun nahiyar turai (UCL) na 2017/18 a makon da ya gabata, inda United ta doke kungiyar Basel, da kwallaye 3-0.

Manchester United tayi kira ga magoya bayanta da su daina irin wannan mummunar dabi'a mara kyau domin yin hakan cin mutunci ne ga dan wasan kuma zubda darajan kungiyar ne a idon duniya.

Shidai wannan dan wasa Romelu Lukaku, mai shekaru 24, da haihuwa dan kasar Belgium, bakin fata ne wanda ya dawo kungiyar ta Manchester United, a bana daga kungiyar Everton, akan kudi fam miliyan £75, Kuma ya samu nasarar jefa kwallaye har biyar a wasanni biyar na lig da ya buga wa kungiyar ta Manchester United.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:24 0:00

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG