Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kylian Mbappe Na Iya Zama Dan Wasa Mafi Tsada A Duniya


A yayinda kungiyoyin kwallon kafa da dama irin su Real Madrid ke nuna sha'awarsu ta ganin sun sayo matashin dan wasannan mai shekaru goma sha takwas da haihuwa mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Monaco, mai suna Kylian Mbappe, Kungiyar kwallon kafa dake kasar faransa PSG, ta shiga sahun zawarcin dan wasan inda ta saka masa zunzurutun kudi har fam miliyan £119 don ganin ta mallakeshi.

Idann har haka ya kasance Mbappe, zai zamo dan wasa na daya da yafi kowa tsada a duniyar kwallon kafa inda zai dara kan Paul Pogba na Manchester United wanda a yanzu shine kan gaba wajan tsada fam miliyan £89.

Hukumar gudanarwa ta kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, ta ce zata yi kokarin taga ta sayi manyan 'yan wasa a kakar wasan bana kamar yadda mai horas da kungiyar Arsene Wenger, ya bukata.

Leicester City, tana zawarcin dan wasan gaba na super Eagles, na Najeriya mai taka leda a Manchester City, Kelechi Iheanacho akan kudi fam miliyan 25

Liverpool tace dan wasan Borussia Dortmund Aubameyang zai jamata kudi kimanin fam miliyan £63 kafin ta kawoshi kungiyar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:22 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG