Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwararrun Masu Ninkaya Ne Suka Gano Matasa 12 Makale A Kogo


Kwararrun masu ninkaya sun ba matasa goma sha biyu ‘yan kwallon kafar kasar Thailand da kuma mai horas dasu da suka makale a wani kogo, kwayoyin magunguna masu kara karfi domin taimakonsu murmurewa yayinda ake tunanin hanyar da za a maidasu gida.

An samu matasan goma sha biyu ‘yan wasan kwallon kafa na kasar Thailand da mai horror da su da rai cikin wani kogo, kwanaki goma bayan sun bace.

Jiya Litinin gwamnan lardin Chiang Rai, Narongsk Oscthanakcon ya fadawa manema labarai cewa, “Mun samo dukansu goma sha uku lafiya, mun yi ta tafi dukanmu muna murana, sun tagayyara ainun bayan shafe kwanaki tara babu abinci, amma suna nan lafiya sai ‘yan kananan ciwuka da suka ji kawai.

Su wadannan matasa 'yan shekara tsakanin sha daya zuwa sha shidda da mai horon su, mayakan ruwa na musamman ne suka same su makale cikin kogo jiya Litinin.

A wani hoton bidiyo mai tsawon minti biyar da masu aikin ceton suka ba kafofin watsa labarai, an nuna matasan sanye da kayan wasansu, sun zauna a kasa kusa da makeken ruwa. Da alama hasken fitilar masu aikin ceton tana kashe masu ido.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG