Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ku Daina Kyamar Masu Tabin Hankali - Inji Yarima Harry


Yariman masarautar Britaniyya Harry, tare da matar shugaban Amurka Michelle Obama da likita Jill Biden, matar mataimakin shugaban Amurka, sun hadu a wani sansanin dakarun Amurka don yin fadakarwa akan shirye-shiryen da za su taimakawa jami’an tsaron da suka jikkata.

Yariman ya yi kira ga jama’a da su daina kyamatar matsalolin da suka shafi tabin hankali, ba ma kawai a bangaren tsoffin soja ba, har ma da tsakanin sauran al'umma.

“Tsoron kyamar da ke tattare da abubuwan da su ka shafi batan hankali, na daya daga cikin kalubalen da tsoffin jami’an tsaro ke fama da su a yau. Sauran jama’a ma na fama da ire-iren matsalolin kamar dimuwa da firgita bayan aukuwar wasu munanan lamura a rayuwarsu, da kuma jin tsoro, da rashin jin dadin rayuwa. Akwai bukatar mu taimaka masu samun duk wani goyon baya da suke bukata, “ a cewar yarima Harry.

Yariman kuma tallata wasu wasannin na kasa-da-kasa, da sojojin da suka jikkata a fagen daga ke yi.

Harry ne ya ja ragamar wannan wasan karon farko da aka fara shi a birnin London cikin shekarar da ta gabata.

XS
SM
MD
LG