Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaki Na Haifar Da Muggan Haddura Ga Rayuwar Dan'adam


Suga Ga Jikin Dan'adam
Suga Ga Jikin Dan'adam

Shan zaki ba wai kiba kawai yake sawa ba, harma da wasu cututtuka da mutane basu ganewa. Sau nawa mutane ke sanin yawan adadin suga da suke sama jikin su? A lokkutta da dama mutane kan ci abubuwa dake dauke da zaki, kamar su, Ice cream, minti, dama sauran su. To abun tambaya a nan shine, mutane na kwatanta yawan suga dake cikin wadannan abubuwan da sukan sha?

Mafi illa daga ciki shine, yadda wasu kan dauki cin abubuwa masu dauke da zaki wani abun gwaninta ko abun yi, da dama wadannan shaye-shayen da ciye-ciyen marasa amfani da kuma rashin lura suke haifar da kiba, ciwon hanta, ciwon daji, da dai wasu muggan cututtuka.

A wasu lokkuta akan kai mutun asibiti wanda wasu cuttukan ma ba’a iya gane su, kana mutane da dama basu ayyukan motsa jiki balle wannan zakin yakone. Musamman ga matasa, hakan na da matukar illa gare su, babu kamar idan suka dauki shan zaki sana’a, sai sun kai wani matsayi na shekaru kana zakin yafara tambayar su. A cewar wasu kwararru a fannin kiwon lafiya, suga da ake sawa a cikin irin abinci da mutane ke ci, tana da matukar illa ga rayuwar dan’adam. Don haka akwai bukatar mutane su guji hakan.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG