Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nan Gaba Jirgin Saman Drone Zai Rika Kai Maka Kayan Da Ka Saya A Kanti Zuwa Gida


Kantin sayar da kayayyaki mafi girma a duniya, Wal-Mart, ya nemi izni daga hukumomi na Amurka domin yayi gwajin amfani da jiragen sama marasa matuka wajen kai ma jama’a kayan da suka saya gidajensu, da daukar kaya daga gefen kanti da kuma lissafin kayayyakin dake ajiye a dakunan ajiye kayayyakinsa.

Wannan alama ce dake nuna cewa kantin Wal-Mart yana shirin karawa da kamfanin sayar da kayayyaki ta intanet, Amazon, wanda shi ma ya fara shirin yin amfani da jiragen Drone domin kai wa mutane kayayyakinsu har gida.

Kamfanin Wal-Mart yayi wata da watanni yana gwajin yin amfani da kanana jirage marasa matuka a cikin dirka-dirkan dakunan ajiye kayayyakinsa, kuma a yanzu a karon farko yana neman iznin yin gwajin jigilar kaya da wadannan kayayyaki a waje.Kamfanin yana shirin yin amfani da Jiragen saman Drone kirar wani kamfanin kasar China mai suna SZ DJI Technology.

Kwafen takardar neman iznin da kantin Wal-Mart ya mika ma Hukumar Kula da Zirga-Zirgar Jiragen Sama ta Amurka, ta nuna cewa a bayan yin amfani da jiragen saman Drone wajen lissafin kayayyakin da motocin daukar kaya suka kawo zuwa dakunan tara su da kuma wasu ayyukan inganta yadda ake rarraba kayayyakin, kamfanin yana son a ba shi iznin gudanar da bincike kan yadda zai iya yin amfani da wadannan nau’in jiragen sama wajen kai kaya ga mutanen da suka saya zuwa kofar kantin, ko kuma kai musu har gidajensu.

Wannan mataki na kantin Wal-Mart yana zuwa a daidai lokacin da Amazon.com da Google da wasu kamfanoni suka fara gwajin jiragen saman Drone bisa tsammanin cewa nan ba da jimawa ba Hukumar kula da Zirga-Zirgar Jiragen Saman Amurka zata fito da dokoki da sharrudan yin amfani da irin wadannan jirage domin harkokin kasuwanci nay au da kullum.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG