Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kocin Tawagar Jamus Ta Soki Hukumar FIFA


Alex Morgan World Cup
Alex Morgan World Cup

Mai horar da ‘yan wasan kwallon kafar Jamus, Silvia Neid ta soki hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA da ta hada abokiyar karawarta ta Amurka a Otel guda, yayin da ‘yan wasan ta ke shirin karawa a zagayen kusa da na karshe da kasar ta Amurka a gasar cin kofin duniya ta mata da ake yi Canada.

A cewar Kocin ta Jamus, bai kamata a hada kungiyoyi biyu da za su kara da juna a Otel guda ba, tana mai cewa ba a haka a gasar cin kofin duniya ta maza.

Silvia mai shekaru 51, wacce kuma tsohuwar ‘yar wasan Jamus ce, ta kara da cewa ba a wannan karo ne kadai ba, kusan a baki dayan gasar abin da ke faruwa ke nan.

Ta kuma ce sun fuskanci mawuyacin hali a ce bayan sun doke ‘yan wasan Sweden, wanda suka harzuka, a ce kuma sun zo suna hawa gurgar hawa gidan sama Tare, lamarin da ta ce hakan bai dace ba.

A nata bangaren, mai horar da ‘yan wasan Amurka Jill Ellis itama ta nuna hakan bai dace ba, ta kuma kara da cewa wata rana saura kadan ta shiga dakin cin abincin ‘yan wasan Jamus.

XS
SM
MD
LG