Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Carlos Bacca Zai Koma AC Milan


AC Milan coach Massimiliano Allegri gestures during a Champions League, Group H, soccer match between AC Milan and Ajax at the San Siro stadium in Milan, Italy, Wednesday, Dec. 11, 2013. (AP Photo/Antonio Calanni)
AC Milan coach Massimiliano Allegri gestures during a Champions League, Group H, soccer match between AC Milan and Ajax at the San Siro stadium in Milan, Italy, Wednesday, Dec. 11, 2013. (AP Photo/Antonio Calanni)

Carlos Bacca dan wasan kungiyar Sevilla, ya amince da wata yarjejeniya ta komawa kungiyar AC Milan.

Wakilin Becca Sergio Barilla ne ya tabbatar da cewa ‘dan wasan ya zabi AC Milan a matsayin kulub din da zai bugawa wasa daga cikin sauran kungiyoyin da suke nemansa.

Alokacin da yake magana da wani gidan jarida Becca yace, “dole wannan lamari ya zo karshe, saboda a kullum ana alakantani da kungiyoyi daban daban, amma yanzu gaskiyane na amince yarjejeniya da AC Milan. Nayi magana da su wakilina yayi magana dasu mun yarda da yarjejeniyar, wannan gaskiya ne.”

Ya ci gaba da cewa wannan kulub ne da muke da tabbacin zai dauke ni dari bisa dari, amma har yanzu dai ban saka hannu a kan kwantaragi ba.

Becca dai ya zarga kwallaye har biyu a wasan karshe cin kofin kalubalen Turai da akayi, wanda ya taimakawa kulub dinsa Sevilla samun nasarar zama zakaran wasan, ya kuma ‘kare kakar wasan da kwallaye 20.

XS
SM
MD
LG