Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ni Dan Takara Ne -Inji Maradona


Italy Maradona
Italy Maradona

A cewar wani marubuci kuma dan jarida Victor Hugo Morales, wanda ya kaddamar da wani shirin talabijin da tsohon dan wasan kwallon kafa Maradona a lokacin da ake buga wasan cin kofinn duniya a shekarar da ta gabata, dan wasan ya tabbatar masa da niyyar sa.

Morales ya rubuta ta kafar yada labarum Tweeter cewar “ya fada mani cewar zai tsaya takarar shugaban cin hukumar kwallon kafa FIFA kuma ya bani dama da in bayyana hakan” .

“ni dan takara ne’ kalamun da Diego Maradona yayi anfani da su Kenan wajan amsa tambayar da na yi masa a game da gabatar da wadanda az su tsaya shugabancin na FIFA.

Maradona ya soki shugaban na FIFA Sepp Blatter karara, inda yay a kira Sepp Blatter shugaba mai mulkin kamakarya, ya kuma kara da cewa ya mayar da hukumar ta FIFA wurin rashawa.

Blatter da ya ce zai yi murabus kawanaki kadan bayan sake zaben sa da aka yi karo na biyar a sakamakon matsalar cin hanci da rashawa

XS
SM
MD
LG