Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

In Da Gaske Ne, Lallai Keshi Ya ci Amana -Inji Igbokwe


Stephen Keshi
Stephen Keshi

Daya daga cikin manyan jami'an kwamitin ladabtarwa na hukumar kwallon kafar Najeriya NFF Iyke Igbokwe, ya bayyana cewa idan aka sami tabbacin cewa mai horar da 'yan wasan Najeriya Stephen Keshi da laifin neman aikin horar da 'yan wasan kasar cote d'Ivoire to lallai za'a sallame shi.

Sai dai yayin da ya gurfana a gaban kwamitin ranar talatar da ta gabata, Keshi ya musanta wannan zargi, amma duk da haka hukumar ta NFF ta kaddamar da bincike kan wannan lamari, inda mai yiwuwa ta ce zata tura wata tawaga zuwa Abidjan babban birnin kasar domin gano gaskiyar lamarin.

Shugaban NFF Amaju Pinnick ya bayyana lamarin a matsayin kasada idan har Keshin na neman aikin duk da cewa ana biyan shi albashin sa akan kari.

Igbokwe ya kara da cewa idan dai har Keshin yana neman wannan aiki da gaske to tamkar cin amana ne. Stephen Keshi dai yana da kwantaragin horar da 'yan wasan Super Eagles na shekara biyu wanda aka sabunta a bayan kwantaragin sa na shekaru uku.

Ga karin bayani.

XS
SM
MD
LG