Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasuwar Zaratan 'Yan Wasan Kawallon Kafa Na Ci Gaba Da Habaka


Kungiyar kwallon Kafa ta Chelsea ta bayyana cewar babu wata kofa ga dan wasanta Eden Hazard, na barin kungiyar don komawa kungiyar Manchester united a yanzu.

Chelsea ta fadi hakanne bayan da wasu magoya bayan kungiyar suke rokon sa da ya koma wasa a karkashin tsohon Kocinsa Jose Mourinho wanda yanzu yake kungiyar Manchester united.

Har ila yau dan wasan gaba na Chelsea, Alvaro Morata, mai shekaru 25, na shirin barin kungiyar dan komawa kulob din Juventus, inda ake ganin Chelsea zata mai da hankalinta wajan ganin ta dauko dan wasan PSG Edinson Cavani, dan shekaru 31 da haihuwa.

Arsenal tana yunkurin ganin ta dauko Kocin Juventus, Allegri ko kuma tsohon Kocin Barcelona Luis Enrique, don kasance mata koci a shekara mai zuwa sai dai a gefe guda duk kansu suna duba yuwar zuwansu domin yanayin tsare tsare na hukumar gudanarwa ta Kungiyar ta Arsenal.

Haka kuma Kungiyar ta Arsenal ta ce tana da karfin gwiwar cewar dan wasanta Jack Wilshere, zai sabunta kwantirakin sa don cigaba da zama a kungiyar

Kungiyar Bayern Munich ta ce a shiye take da ta sayar da dan wasan gabanta dan kasar Poland Robert Lewandowski, wanda Manchester united da Real madrid ke da burin ganin sun dauko shi a karshen kakar wasan bana.

Shugaban kungiyar kwallon Kafa ta Barcelona ya ce kulob din ya fara tattaunawa da dan wasanta Samuel Umtiti, kan sabunta kwantirakinsa a kungiyar kasancewar Manchester united, ta nuna sha'awarta kan dan wasan mai shekarun haihuwa 24 a duniya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:50 0:00


  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG