Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muhammad Salah, Da Wasu Zakaru Sun Samu Lambar Yabo


Danwasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Liverpool dan kasar Masar Mohammad Salah, mai shekaru 25 da haihuwa ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na bana wadda kungiyar marubuta labarin wasannin kwallon ta saba bayarwa duk shekara.

Salah ya samu wannan nasarar ne bisa irin kokarin da yayi a kakan wasa da muke ciki inda ya taimaka wa kungiyarsa ta Liverpool, a wasanni bana, danwasan ya zurara kwallaye 31, a wasanni 34 da ya buga wa kungiyarsa ta Liverpool a Firimiya lig na Ingila a dukkannin wasannin da ya buga a wannan shekara ya zurara kwallaye 43.

Kuma shine danwasan kwallon kafa na farko da ya taba lashe wannan lambar yabon daga nahiyar Afirka. Danwasan tsakiya na Manchestery City
Kevin de Bruyne shi ya zo na biyu.

Sai danwasan gaba na Tottenham Harry Kane a matsayi na uku, sauran yanwasan da suka samu kuri'a daga kungiyar na marubuta Labarin wasannin kwallon kafa, sun hada da Sergio Aguero (Man City), Christian Eriksen (Tottenham), Roberto Firmino (Liverpool), Nick Pope (Burnley), David Silva (Manchester City), Raheem Sterling (Man City)da kuma Jan Vertonghen na kungiyar (Tottenham).

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG