Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Magoya Bayan Arsene Wenger Sama Da Dubu 60 Sanye Da Jajayen Kaya Wajan Ban Kwana


Rahotanni na cewar an garzaya da tsohon Kocin Manchester united Sir Alex Ferguson asibiti cikin gaggawa inda za a yi masa aiki a kwakwalwarsa.

Kwac-kwac da dama a duniya sun tura sakonninsu na nuna juyayi da fatan samun sauki kan rashin lafiyar dake damun Sir Alex Ferguson, cikin su harda Kocin Arsenal mai barin Gado Arsene Wenger, inda shima ya tura da sakon samun sauki ga takwaransa Tsohon Kocin Manchester united Sir Alex nan rashin lafiyar da ya ke fama da ita.

Idan ba a manta ba, a satin da ya gabata ne Sir Alex Ferguson, ya mika kyauta ta musamman ga Wenger a wasan da Manchester united, ta doke Arsenal 2-1 a wasannin Firimiya lig na bana.

Bayan haka kuma a jiya ne Kocin Arsenal, Arsene Wenger ya yi bankwana da magoya bayan kungiyar a wasansa na karshe da ya buga a filin wasa na Fly Emirates, bayan da ya shafe shekaru 22 jimillar kwanaki 7,876 kenan a matsayin sa na manaja a kulob din inda ya lallasa Burnley da ci 5 -0 a wasan Firimiya lig mako na 37, wanda hakan ya bashi samun nasara ta 475 a wasanni 826 da ya jagoranci kungiyar Arsenal a gasar Firimiya lig.

Ya samu nasarar lashe kofin Firimiya sau 3 kofin kalu bale na kasar Ingila ( FA Cup) sau 7. Sama da magoya baya dubu 60 ne suke sanye da jajayen riguna a wasan na ranar lahadi da aka yi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:25 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG