Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Karon Farko, Rohr Ya Yi Magana Kan Tafiyar Victor Moses


Daga karshe dai babban kocin kwallon kafa na Najeriya Gernot Rohr, ya bayyana ra’ayinsa akan aje takalama daga takawa kasar sa leda da daya daga cikin shahararrun ‘yan wasan kwallon na kungiyar Super Eagle, Victor Moses ke shirin yi, inda ya bayyana cewa yana fatan shawarar da dan wasan ya yamke ba aikin baban giwa yayi ba.

Sama da sati guda Kenan da dan wasan na kungiyar Chelsea, ya bayyana niyyar sa ta daina takawa Najeriya, leda inda ya bayyana cewa akwai bukatar ya mayar da hankali wajan bugawa kungiyar sa ta waje wasa.

An riga anyi watsi da maganar kiran dan wasan domin fafatawa a wasannin shiga gasar cin kofin Nahiyar Afirka na shekarar 2019, da za a fara wanda Najeriya zata fafata da Seychelles, a satin da ya gabata, kamar yadda mujallar Daily Trust ta wallafa.

Dan wasan ya takawa kasar sa leda a wasannin cin kofin duniya guda biyu da aka gudanar a shekarar 2014, da kuma na wannan shekarar da aka gudanar a kasar Rasha, kuma a satin da ya gabata ne Moses ya bayyana cewa ya yi murabus daga takawa Najeriya leda.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG