Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Victor Moses Ya Yi Murabus Daga Kungiyar Super Eagles


Victor Moses
Victor Moses

Dan wasan kwallon kafar Najeriya Victor Moses mai shekaru 27 da haihuwa ya bayyana cewa zai yi ritaya daga bugawa kasarsa kwallo.

‘Dan wasan mai taka leda a kungiyar Chelsea ya bugawa kasarsa kwallo har sau 37, ya kuma zarga kwallaye a raga har 21.

A cewar Victor yaji dadin bugawa kasarsa kwallo, kuma lokacin da yake sanye da rigar kungiyar Super Eagle akwai wasu abubuwan Alheri da suka faru da shi wadanda ba zai iya mantawa da su ba a rayuwarsa.

Ya kara da cewa ina ganin yanzu lokaci ya yi da zan ajiye takalmana, domin na mayar da hankali akan Kulob dinsa.

Shi dai Moses ya samu nasarar cin kofin nahiyar Afirka da Najeriya a shekarar 2013, kuma ya bugawa Najeriya kwallo har sau biyu a wasnnin cin kofin duniya na shekarar 2014 da 2015.

An fitar da Najeriya a wansannin rukuni-rukuni a Rasha, bayan da suka cinye kungiyar Iceland amma suka sha kasha a hannun Croatia da Argentina.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG