Shin ko mutane sun shirya hawa jirgin sama da bashi da matuki wato pilot? Wannan fasahar ta tabbata amma babu kamfanin dake tunanin yin amfani da ita a yanzu haka.
Idan aka duba yadda ake samun munanan hatsarin jiragen sama, a satin daya wuce ne jirgin saman Germanwings ya fado ya dagargaje kan dutsen Alph wanda babu dutse mai tsayinsa a duk fadin Turai, wanda ake zargin ‘daya daga cikin direbobin jirgin ne ya haddasa.
Hakan ne yasa mutane suka fara tambayar shin barin jirgin ya tuka kansa ba zai fi alkhairi ga ‘dan Adam ba? Wasu masana sun ce barin jirgi ya tuka kansa zaifi aminci ga mutane.
Mary Cummings, wata tsohuwar matukiya jirgi ce kuma farfesa ce mai koyar da injiniya a jami’ar Duke dake Amurka, tace “jirage suke tuka kansu a yanzu haka,” ta kuma bayyana cewar duk matuka jirgin sama na tukin minti uku ne kacal a duk inda zasu a duniya, kuma basu bukatar yin hakan. Ta kara da cewa, kimanin kashi tamanin cikin dari na hatsarin jirgin sama da ake samu na faruwa ne dalilin kuskuren ‘dan Adam.
Kasar Amurka na amfani da jiragen yaki da basu da matuka, wanda girmansu yakai kusan girman jiragen jet dake ‘daukar fasinja 737. Rahotannin rundunar sojan Amurka na nunin jiragen marasa matuki basu fiya hatsari ba, kamar na jiragen dake da matuki.