Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gangamin Fita Zabe A Jihar Taraba


Shugaban hukumar zabe ta Najeriya, Farfesa Attahiru Jega
Shugaban hukumar zabe ta Najeriya, Farfesa Attahiru Jega

Yayin da ya rage kasa da mako guda a gudanar da zabe gwamnoni a Najeriya, wani alkalamin hukuamr zaben kasar ta INEC ya nuna cewa mutane da dama ba su fita yin zabe a wasu yankun na Jihar Taraba ba.

Hakan dai ya sa shugabannin al’uma suka gudanar da gangamin fadakarwa domin a samawa jihar makoma mai kyau.

“A yi kokari a zbi shugabannin adilai a yi kokari a zabi wadanda suke cikin adilai, a dubi gayyara mutanen da aka sansu da adalci a zabesu.” In ji Dr. Ibarhim Jali, daya daga cikin shugabannin addinan kasar.

Yanzu haka shugabannin al’umomi daban-daban na ci gaba da yin kira ga mabiyansu da su fita kwansu da kwarkwatansu domin kada kuri’unsu.

“Ina kira ga al’umar Fulani da su fita su yi zabe, su ba da kuri’a, su zabi abinda ya fi mana Alheri.” In ji Hardo Ibrahim Mutum biyu.

Yanzu haka jam’iyar PDP na ikrarin cewa ita za ta lashe zaben gwamnan jihar yayin da APC ke nuna akasin hakan.

“Hasashen ya nuna cewa dan takararmu shi zai lashe zabe, na farko zaben da aka yi na shugaban kasa PDP ce ta lashe zaben a jihar.” In ji Hassan Karofi dan jam’iyar PDP.

To sai dai APC ana ta banagren ta ce ba haka lamarin ya ke ba “a yanzu bamu da mafita illa Hajiya Aishatu Jummai Alhassan, muna ganin itace za ta zo ta gyara al’muran domin batun addini da kabilanci yay a bata siyasar Taraba” In ji Malam Salisu Bawa wani dan jam’iyar APC.

XS
SM
MD
LG