Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kaftin John Terry Na Shirin Ajiye Takalmi, Zai Yi Murabus


Tsohon kaftin din tawagar Kungiyar kwallon kafa ta Ingila da Chelsea John Terry ya yi ritaya daga kwallon kafa. Terry, mai shekaru 37, da haihuwa bai kasance tare da wata kulob ba tun lokacin da ya bar Kungiyar Aston Villa a gasar zakarun Turai a lokacin rani.

Tsohon Mai tsaron gidan ya sanar da ajiye takalman taka ledan sane ta kafar sada zumuncin sa Instagram yana cewa: "Bayan shafe shekaru 23 a matsayin dan kwallon, Na yanke shawarar yanzu shi ne lokaci Ya dace don in yi ritaya daga wasa in bar wa matasa don su nuna irin tasu bajintan.

John Terry, ya yi wa kasar sa ta Ingila wasanni har 78, ya bar Chelsea
a shekara ta 2017 bayan shekaru 20 da ya shafe a kulob din.

​Inda ya samu Nasarar daukan kofin Premier na kasar Ingila har sau biyar, kofin FA guda biyar, A gasar zakarun Turai a lokacinsa a Stamford
Bridge, Ya zama danwasa a kulob din mafi iya ado inda ya buga wasanni sama da 700 wa Kungiyar ta Chelsea a tsawon shekaru 20 da yayi.

John Terry ya buga wasannin 2017-18 a Aston Villa kuma wasan karshe shine wasan na Neman shiga gasar zakarun Turai da Fulham Mayu. A yanzu haka dai ana alakanta danwasan da cewar zai koma matsayin mai horas da yan wasa wadda ba'a baiyana sunan Kungiyar ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

  • 16x9 Image

    Daula Saleem

    Daula Saleem, Ma’aikaciyar Jarida ce (International Broadcaster - Multimedia) a Sashen Hausa na Muryar Amurka dake birnin Washington, D.C. Yar asalin Jihar Katsina. Ta karanta aikin Jarida a Jami’ar Bayero University Kano.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG