Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Zargi Ronaldo Da Ba Wata Hakuri Bayan Yi Mata Fyade


Shahararren dan wasan kwallon kafa na Duniya Cristiano Ronaldo, ya fadawa matar da ake zarginsa da yiwa fyade "yi hakuri ni mutumin kirki ne" yayinda ya yi mata fyade bayan sun gama shagali a Las Vegas, a cewar takardun kotun da ke sauraren karar.

Mujallar New York Post, ta wallafa cewa Dan wasan wanda ya ce labarin kanzon kurege ne da kuma kage, ya biya matar da ake zarginsa da yiwa fyade kudi sama da dalar Amurka $350,000, a shekarar 2010 domin toshiyar baki, kamar yadda mujallar UK Sun ta wallafa.

Yanzu haka lauyoyin da ke kare matar sun daukaka kara akan tauraron dan wasan ranar juma'a da ta gabata wata kotu dake jihar Nevada, a kasar Amurka.

Matar mai suna Kathryn Mayorga, ta yi ikirarin Ronaldo ya yi mata fyade bayan sun hadu a wani otal da ake kira Las Vrgas Palms Hotel and Casino a shekarar 2009. Ta bayyana cewa ta je wurin 'yan sanda a washe garin afkuwar lamarin amma lauyan ta ya bata shawarar yin sulhu a lokacin.

Jami'an 'yan sandan jihar Vegas zasu ci gaga da gudanar da bincike akan zargin wanda ya hada da cewar Ronaldo ya nuna mata tsiraicinsa kana ya fada mata a wani daki a otal din.

"Abin da suka fada yau karya ne, labarin kanzon kurege ne kawai" zakaran dan wasan kwallon ya fada a wanmi hoton bidiyo da aka wallafa a shafin Instagram.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG