Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Diego Costa Ya Ce Ya Yi Da Ya Sani


Tsohon dan wasan gaba na kungiyar ‘yan wasan kwallon kafa ta Chelsea, Diego Costa, ya bayyana dalilin sa na cewa da ya sani da bai koma kungiya da taka leda ba, ya ce "na yi matukar da na sani".

Coasta ya kwashe kakar wasanni hudu a tsohon kulob din sa kafin ya koma kungiyar Chelsea a shekarar 2014, inda aka yi musayar sa akan zunzurutun kudi Fam Miliyan 32.

Cikin shekaru hudu da ya kwashe a kungiyar Stanford Bridge, Costa ya lashe kofunan wasannin Premier League guda biyu.

Karshen wasansa a kungiyar kungiyar Chelsea ya zo ne yayin da ya sami sakon kar ta kwana daga Conte, wanda ya fada masa cewa bashi da makoma mai kyau a kungiyar.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG