Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jarumin ‘Daukar Hotan Bidiyo Na Fina Finai Isma’il M Isma’il


Isma'il Mohammed Isma'il
Isma'il Mohammed Isma'il

Dandalin VOA ya ziyarci Isma’il Mohammad Isma’il, mai daukar hotan bidiyo na fina finai inda ya bayyana mana cewa bayan daukar hotan bidiyo na fina finan Hausa na Kannywood yana ‘daukar na Turanci ma wato na masana’antar Nollywood.

Isma’il dai shine daraktan ‘daukar hotan bidiyo a wadannan masana’antu, wakiliyar Dandali Baraka Bashir ce ta samu zantawa da shi lokacin da ta ziyarshe inda suke hada wani sabon wasan Hausa a gidan ajiye namun daji wato gidan Zoo.

Ya kuma ce yana da sha’awar duk wani abu da ya shafi hoto a rayuwar sa tun yana karami wato tun yana makarantar firamare, har Allah yasa ya girma ya kuma cimma burin sa na yin abinda yake so a matsayin sana’ar sa.

Isma’il ya kwashe a kalla shekaru goma sha biyar zuwa sha takwas yana wannan sana’ar.

XS
SM
MD
LG