Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'ar Jahar Kwara Ta Kori Dalibai 108


Rahotanni daga jami’ar Illorin jahar kwara sun bayyana cewa hukumar makarantar ta bada sanarwar korar sababbin dalibai 108 a sakamakon shiga makarantar da takardar karatu ta bogi. Shugaban makarantar Farfesa Abdulganiyu Ambali ya bayyanawa kwamishinan ‘yan sanadan jahar Mr Sam Okaula ne a yayin da ya ziyarce shi.

Farfesan ya kara da cewa saboda yadda ayyukan makarantar suka kankama da kuma ingantuwar tsarin karatu a jami’ar ne yasa samun takadar karatu a makarantar ya kasance mai matukar wahala.

Shugaban y aba kwamishinan ‘yan sandan tabbacin ci gaba da aiki tare da sJami’an tsaron domin tabbatar da gudanar da ayyuka cikin aminci. kuma ya kara da cewa jami'ar zata cigaba da ba 'yan sandan hadin kai da kuma dukkan bayanan da suke bukata domin gudanar da ayyukan su.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG