Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Cafke Wani Matashi Dan Shekaru 18 Da Makamai A Jihar Taraba


Rundunar ‘yan Sanda ta jihar Taraba ta cafke wani matashi da shekaru goma sha takwas da muggan makamai da albarusai.

Wata rundunar ta masamman da aka kafa a jihar akan makamai ne ta cafke matashi da wasu mutane da ake zargi da aikata laifuffuka kama daga fashi da makami, satar mutane da satar Shanu.

Kwamishinan ‘yan Sandan jihar ta Taraba Shaba Alkali, wanda ya tabbatar da batun a lokaci da yakewa ‘yan jarida jawabi, yace an kara samun nasara wajen yaki da laifuffuka tunda aka kafa runduna ta masamman na yaki da makamai da taimakon kungiyar .yan sintiri da jama’ar gari.

Yakara da cewa hada kafi da karfe tsakanin ‘yan Sanda da masu sintiri da jama’ar gari ya taimaka gaya wajen cimma nasarar da aka samu akan yaki da aikata laifuffuka a jihar Taraba.

XS
SM
MD
LG