Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zababbun Garuruwa Da Sukafi Tsafta Da Kayatarwa A Najeriya


A duk lokacin da ake maganar garuruwa masu kyau a duniya, ba shakka idan aka zo yankin kasashen Afrika, sai an duba wasu garuruwa a Najeriya, da suka shiga cikin jerin garuruwa masu kayatarwa da tsari. Najeriya na daya daga cikin kasashe da Allah, ya azurta da arzikin duwatsu, manya-manyan tsaunuka, itatuwa, da yanayin ruwan sama, yanayin bazara da na kaka.

Hakan yasa an zabo wasu garuruwa, da suka cika duk matakai da ake amfani da su wajen, bayyanar da tsari da kayatarwa. Babban brining jihar Lagos, shine gari na farko da yafi kyau a kasar Najeriya. Haka garin babban brnin tarayya Abuja, shine gari na biyu. Haka garin Calaba, a jihar Cross River. Sai gari na hudu shine garin Jos, a jihar Plateau.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG