Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fiye Da Kashi 80 Cikin 100 Na ‘Yan Majalisun Tarayya Da Gwamnoni An Zaben Su Dalilin Buhari Ne


Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Gamayyar kungiyar matasa ta jihar Filato, ta koka da rashin tuntubar jama’ar Najeriya kafin Karin kudin Man fetur da Gwamnatin Najeriya tayi da cewa shi ke kawo ce ce ku ce.

Shugaban kungiyar Shamaki Peter, ne ya bayana haka a wani hira da muryar Amurka, yana mai cewa yakamata ace Gwamnati ta fadakar da jama’a kafin ayi Karin wanda hakkan zai sa jama’a su fahimci dalilin dake tattare da matakin da Gwamnati ta dauka.

Ya kara da cewa fiye da kashi tamanin a cikin dari na ‘yan majalisun tarayya da Gwamnoni an zaben sune saboda shugaba Muhammadu Buhari, don haka idan irin wannan ya tasu yakamata shugaba Buhari ya yiwa ‘yan Najeriya, bayani da kansa na irin matakin da Gwamnati ke son dauka da irin taimakon da Gwamnati ke bukata, daga jama’a.

Kungiyar ta bukaci Gwamnati da ta yiwa jama’ar kasa bayani kan abinda zata yiwa jama’a, a madadin tallafin da aka janye kama daga gina rukunin gidajen masu karamin karfi, motocin sifiri na Gwamnati, samarda magunguna a asibitoci gina wasu ko kuma baiwa matasa gurbin karo ilimi.

XS
SM
MD
LG