Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jama'a Na Yi Mana Mummunar Fahimta- Inji Adam A Adam


Adam A Adam
Adam A Adam

Babban kalubalen da nake fuskanta mussamam idan na shiga jama’a shine yadda ake yi min kallon mutum mara kirki da rashin da’a inji jarumi Adam M Adam.

Ya bayyanawa DandalinVOA hakanne a yau inda ya ce sakamakon yawan fitowa da yake yi a fim a matsayin mara kirki ya haddasa ko fita cikin gari yayi mutane na yi masa mummunan kallo.

Ya kara da cewa da dama sai mutune su rinka gudunsa da zarar ya kusance su, har sai da ta kai shi ga yi musu bayanin cewar su lura a fagen da yake fitowa shiri ne ba gaskiya ba ce, tare da nusar da su cewa wasu hallayar ne da wasuda ake son nusar da alu'umma kuma a mafi yawan lokuta karshen masu ire-iren wadandan hallayar hallaka ne.

Kamar kowannen jarumi Adam ya ce ya shiga harkar fim ne domin ya illimantar kuma ya kara da cewa shi’awa ce ta sa shi harkar fim, Kuma, ya ce burinsa Kannywood ta daukaka har su yi kafada da kafada da Nollywood.

please wait

No media source currently available

0:00 0:07:06 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG