Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutum-Mutumi Ya Doke Dan'adam A Wasan Kwallon Table Tennis


Taron gwanayen kirkirar mutunmutumi da aka gudanar a birnin Las Vegas, an gabatar da mutunmutumi ‘Robot’ mai ban al’ajabi, da yafi duk wasu robot basira, domin kuwa wannan mutun-mutumin yana buga wasan table tennis.

An buga wasa tsakanin mutum-mutumin da dan'adam, haka wani mutum-mutumi ya buga wasan ‘Scrabble’ wato dara da mutun, mafi yawancin kanfanonin kimmiyya da fasaha na duniya, suna yunkurin kirkirar mutum-mutumi da za’a inganta shi da basirar zamani.

Babban burin wadannan kamfanoni shine su kirkiri mutum-mutumi da ka iya zama cikin dangin mutane, yayi rayuwa kamar yadda ake da ‘ya’ya, a takaice yana iya cike gurbi ya zama kamar yadda mutane ke yi da ‘ya'yan su.

Ire-iren mutum-mutumin da aka gabatar a wajen bajekolin suna da hallitu irin na mutun, babu wani abu da mutun zai yi da basu yi, kamar kyabta ido, girgiza kai, bude baki, da dai makamantansu.

Wani daga cikin mutum-mutumin kuwa har ma da hamma yanayi, haka kuma sukan yi magana da wasu yaruka daban daban, kana suna karya harshe don kwaikwayon maganar wasu.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG