Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Fina-Finai Ta Yafewa Rahama Sadau Kuwa


Rahama Sadau
Rahama Sadau

Jaruma Rahma sadau ta bukaci masoyanta da masu ruwa da tsaki su yi hakuri dangane da abin da ya faru a baya, inda ta ce idan abu ya faru afuwa ya kamata a yi mata kamar yadda ake wa kowane dan'adam ta kuma kara da cewa kamar sauran 'yan adam, ita ma zata iya yin kuskure.

Ta bayyana wa manema labarai haka ne inda ta ke nemi a yafe mata kura-kuranta.

A dai makon jiya ne daraktan hukumar tace fina finai da dab’u ta jihar Kano Ismaila Na’abba Afakallah, ya ce hukumar ta yafe wa jaruma Rahma Sadau dangane da laifin da ta aikata.

Ya kara da cewa duk lokacin da wani mutum yayi abu na laifi ya kuma ya fito ya nemi a yafe masa akan abinda ya aikata, ya nemi afuwa, kuma ya kamata a duba akuma yafe masa , inda ya ce ta je hukumar domin neman gafara, ya kuma bukaci ta bi wasu ka'idoji kafin a yafe mata.

Shugaban ya ce Rahma ta bi dukkan sharuddan da aka gindaya mata , sa'annan yanzu hukumar tace fina-finai zata duba wasu daga cikin ayyukanta

Amma ba haka abun yake ba ga kungiyar masu shirya fina-finan Hausa ta kasa wato MOPPAN, domin jami'i mai kula da harkokin hulda da jama'a na kungiyar Balarabe Murtala Baharu, ya ce a iya saninsu har yanzu ba’a yafe wa Rahma Sadau ba.

Ya kuma kara da cewa abinda hukumar tace fina-finai ta yi daidai ne, amma ba hukumar ce ta ce ta kori Rahma Sadau ba, kuma a wannan lokaci ne aka kafa kwamitin da zai duba batun Rahma.

Jarumar ta rubutu wasika, haka kuma kungiyar MOPPAN ta nemi jarumar ta gurfana a gabansu amma sai ta ce bata Najeriya a lokacin har sai watan Fabrairun wannan shekara, zata dawo, inda kungiyar MOPPAN ta ce sai ta zo gaban kwamitin sa'annan za a yafe mata. Toh yanzu dai shawara ga rage ga mai shiga rijiya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:04 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG