Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Inda Siyasar Addini ke Tasiri a Najeriya


Matasa sun taru suna wakoki
Matasa sun taru suna wakoki

An yi kira ga dattawan Najeriya, masamman na arewa dasu ja baya domin baiwa matasa damar jan ragamar shugabanci, wani matashi Idris Ahmad Tijjani, ne ya furta haka a wata hira da wakilin muryar Amurka, Saleh Ashaka.

Yace “zaka ga dattawa da suka yi siyasa fiye da shekaru talatin har yau suna neman mukami a Gwamnati, kuma wannan abun bayyiba in har baza ayi canji ba Arewa bazata ci gaba ba shi ya sa muke neman tsofaffin nan su hakura sun tamaka da adu’a, su baiwa matasa dama domin samun canji a arewa.”

Ganin cewa wani lokaci abunda babba ya hango matasa baza su iya hang aba mai zaka ce ?

“Tsofaffin mu da gaske akwai abunda suka hanga wani yaron bazai hanga ba, amma tsofaffin mu girma ya kamasu, yaran yanzu Allah ya bamu basirar iya gudanar da aiki, barin tsoho ya ci gaba da rike mulki shi ya sa talauci yake shigar mu a arewa.”

Ya kara da cewa “ amma duk lokacin da muka ce zamu canza yau ni na ci zamani na gobe kani nay azo ya ci zamanin shi jibi kanin say a ci zamanin shi za’a ci gaba.”

Akan siyasar addini Malam Idris Ahmad, yace siyasar addini na faruwa ne a arewa da kasar Igbo, arewa abunda ke kawo shi jahilci, shi ya kawo mana siyasar addini, mayan zasu je su yaudari talakawa da maganar addini, a duk lokaci da suka ci zabe basu kulla da kowa daga kansu sai iyalansu, yana mai cewa a yanzu haka yayi ragistan kungiya mai zaman kanta domin fadakar da jama’an arewacin Najeriya.

XS
SM
MD
LG