Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Zargin Matashi Jarelu Ahmed Da Kashe ‘Yar Limamin Bauchi


Babban Masallacin Jumma'a na Bauchi
Babban Masallacin Jumma'a na Bauchi

Jami’an ‘yan sandan jihar Bauchi sun kame wani matashi mai shekara 30 da ake zargin ya baiwa yarinya ‘yar shekaru 10 da haihuwa guba har ta kashe ta.

Yarinyar mai suna Hajara Ahmed, yar limamin babban masallacin juma’an jihar Bauchi, Bala Ahmed Baban Inna.

Mai magana da yawun ‘yan sanda DSP Haruna Mohammed, yace ana zargin matashin mai suna Jarelu Ahmed da kashe yarinyar da kuma bunne ta a dakinsa domin gudun kada asirin sa ya tonu. Hakan ya faru ne jiya litinin 31 ga watan Agusta da missalin karfe 6 na yamma.

Mohammed ya fada a wata sanarwa yana mai cewa, “yan sanda sun kame Jarelu Ahmed mai shekaru 30 da haihuwa kan abinda ya faru.”

Ya kuma ce jami’an yan sanda sun ziyarci gurin da abin ya faru, inda aka dauki hotunan gurin tare da aka kuma ‘dauke gawar zuwa babban asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, domin gwaje gwaje. Har yanzu dai ana ci gaba da bincike kan lamarin.

XS
SM
MD
LG