Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Sanda Ya Kirkiro Wata Nau'in Rigar Kare Harsashi


Wani jami'in dan sanda mai suna Godwin Hosea a jahar Bauchi ya sami karin girma zuwa mukamin Sufeto a sakamakon kirkiro wani nau'in rigar kare harsashi da yayi.

A yayin da ake daura masa igiyar mukamin a shelkwatar 'yan sanda da ke garin Bauchi ranar litinin da ta gabata, kwamishinan 'yan sanda Mohammed Mohammed ya bayyaana jami'in a matsayin wanda ya yi anfani da baiwar da Allah ya yi masa.

Ranar 22 ga watan Yulin shekarar 2015 yayin da babban Sufeton 'yan sanda IGP Solomon E A rase ya kai wata ziyara a ofishin 'yan sandan da ke Bauchi jami;in mai mukamin saja ya mika wa shugaban wannan rigar kare harsashi da ya kirkiro a lokacin da shugaban ya gama fareti.

Ganin haka ne nan take sai babban sufeton 'yan sandan ya ya cika da farin ciki sannan ya bayyana karin girman wanda ya ce daga ranar ta 22 ga watan Yuli jami'in ya tashi daga mukamin saja zuwa mataki na gaba wato sufeto.

Wanda ya wakilci kwamishinan 'yan sanda Mr Sumonu Abdumalik, ya yi kira ga jami'in da ya cigaba da sadaukar da kan sa domin yin aiki tukuru da kuma ci gaba da anfani da baiwar da Allah ya ba shi domin ciyar da aikin gaba.

Haka kuma ya yi kira ga sauran jami'an tsaron da su dukufa wajan yin anfani da baiwar da Allah ya basu da kuma kara azama cikin aikin su domin ciyar da aikin gaba da kuma inganta tsaron kasa.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG