Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fati Muhammad: Ina Hada Sana'ar Fina-Finai Da Siyasa


Fati Muhammad

A shirinmu na nishadi a yau DandalinVOA ya karbi bakonci jaruma Fati Muhammad, wacce ta ce a yanzu ta daina fitowa a fina-finai da sunan jaruma, illar dai tana shirya fina-finai ne tare da baiwa jarumai masu tasowa damar damawa da su.

Sai dai wani hanzari ba gudu ba jaruma Fati, a hannu guda kuma ta tsunduma ga harka ta siyasa, take cewa kamar yadda malam Bahaushe kan ce, "Sana’a goma maganin mai gasa" hakan ne yasa ta ga ya dace ta shiga don bada nata gudunmawa.

Fati Muhammad, ta ce tana hada harka ta fim da siyasa kowanne tana bashi damarsa, a cewarta siyasa ne ba wai da niyyar tsayawa takara ba, illar domin daga cikin manufofin wanda take marawa yana da alamun da yakinin tallafawa 'yan fim a sana’arsu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG