Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

China Ta Kirkiro Na'ura Mai Gane Mutum Daga Tafiyarsa


Gwamnatin China ta fara amfani da sabuwar kyamara da aka kayatar da ita da wata na’ura, wadda za ta iya bayyana mutum ba tare da ta ga fuskarsa ba,

Na’urar na amfani ne da yanayin jikin mutun da kuma yadda mutum ke tafiya.

Sabon tsarin zai taimaka wajen gano masu aikata laifufuka, wadanda ke da tunanin ba za'a iya gano su ba, ba tare da an ga fuskokinsu ba ko shatan yatsunsu.

Yanzu haka dai jami’an ‘yan sanda a biranen Beijing da Shanghai sun fara amfani da sabuwar kyamarar mai suna “gait recognition” wannan na daya daga cikin yunkurin kasar China na zamar da kasar ta farko a duniya, da ke da tsarin mai amfani da tsurar basirar dan adam.

Hakan kuma zai ba su damar ajiyar bayanan mutanen kasar ko baki, da wasu masu aikata laiffufuka, shugaban kamfanin Watrix Huang Yongzhen, ya ce na’urar za ta iya gane mutum daga nisan mita 50, kimanin taku (165) daga nesa, koda kuwa mutun ya rufe fuskar shi don kyamarar kada ta gan shi.

Ya kara da cewa ba ma bukatar hadin kan mutane kamin mu iya ganosu, koda kuwa sun bijire muna iya tantance mutu.

Kana babu yadda za’a yi mutum ya yi ma kyamarar wayo, koda mutum ya canza yadda yake tafiya da tunani ba zata iya gane shi ba, na’urar na amfani ne da yanayin gabobin jikin mutun wajen gane kowaye.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG