Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Facebook Ya Kirkiri Wata Sabuwar Manhaja A Shafinsa


Kamfanin Facebook na taka tsantsan wajen kayatar da shafin shi da sabuwar manhaja, da zata dinga ba mutane labaran abubuwan da ke faruwa a yankunansu, a lokacin da suke faruwa. Labarai da suka shafi, sanarwar bacewar mutane, yanayin hatsari ko rufe hanyoyi, aukuwar manya da kananan laifuffuka, ko rufe makarantu da dai sauran su.

Tsarin mai suna “Baki Dayan Yau” “ Today In,” a turance, zai dinga ba mutane labarin abubuwan da ke faruwa a anguwannin su a dai-dai lokacin da suke faruwa, duk lokacin da wani gidan watsa labarai ya wallafa labari, mutun zai dinga ganin su kai tsaye ta shafin shi na Facebook din.

Haka idan gwamnati ta aiwatar da wani hukunci akan abuda ya shafi al’ummah, mutun duk zai ga wannan bayanna a shafinsa, kamfanin ya kaddamar da wannan tsarin ne a garuruwa guda 6 tun a watan Janairu, daga bisani ya kara zuwa 25.

A jiya Laraba tsarin ya fara aiki a kimanin garuruwa 400 na cikin kasar Amurka, da kuma wasu garuruwa a kasar Australia. Wannan yunkurin na Facabook ya biyo bayan zargin da akema kamfanin na taimakawa wajen yada labaran kanzon kurege.

Kokarin kamfanin shine ya maido da martabarsa a idon duniya, da kuma kokarin kyautata dangantaka tsakanin jama’a wanda shine babban makasudin kirkirar shafin tun fil’azal.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jaridar sashen Hausa na gidan radiyon Muryar Amurka (VOA). Dan asalin Hiliya a karamar hukumar Tambuwal, jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG