Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nexus Beats: Kowace Sana'a Tana Bukatar Kwarewa


A cikin shirin DandalinVOA na nishadi a yau, mun samu bakoncin mawaki mai suna Micheal, wanda akafi sani da Nexus Beats. Yace ya fara waka ne bayan da ya fara sana'ar kida ga mawawaka, kuma yau da gobe ce ta sa ya tsinci kansa a fagge na waka.

Nexus Beats, a da dai yana yi wa mawaka kida ne wacce suke dorawa akan wakokinsu, da tafiya tayi tafiya ne ya lura da cewar ya zama lallai ne ya maida hankali domin shima a dama da shi.

Nexus ya kara da cewa a yanzu dai shi komai da ruwanka ne, yana hada waka sannan yakan rubuta wa mawaka waka a wasu lokutanma.

Daga cikin wadanda yayi wa aiki sun hada da su Hazzy Jallabiya, da The Prof sai wanda yayi na yanzu na Son of Jigawa shi ya hada ta.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:12 0:00

  • 16x9 Image

    Daula Saleem

    Daula Saleem, Ma’aikaciyar Jarida ce (International Broadcaster - Multimedia) a Sashen Hausa na Muryar Amurka dake birnin Washington, D.C. Yar asalin Jihar Katsina. Ta karanta aikin Jarida a Jami’ar Bayero University Kano.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG