Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

2face Ya Tofa Albarkacin Bakin Sa Game Da Kama Dammy A Amurka


Shahararren mawakin nan na Najeriya, mai suna Innocent Idibia, wanda aka fi sani da 2face, ko 2baba, ya tofa albarkacin bakinsa a kan kama mawakin nan mai suna Dammy, shi ma daga Najeria, aka kuma garkame shi a jihar Miami ta kasar Amurka, sakamakon zarginsa da aikata laifin satar bayanai da amfani da katin banki na karya.

Yanzu haka Dammy Krane, na fuskantar hukuncin aikata laifuka dai-dai har guda tara, a kotun shari'anta masu aikata miyagun laifuka ta jihar Miami, a kan aikata laifin satar bayanan ajiyar banki wanda yake dai-dai da sata.

Amma da yake jawabi a kafar Talabijin ta mujallar Daily post, ta wallafa cewa 2face, ya musalta mawakin dake garkame a kasar Amurka a matsayin abokin aiki mai cike da hikima da hazaka, kuma matashi sabon jini.

Ya ce "an kama shi ne akan abinda bashi da masaniya a kai sakamakon, mu'amula da lokaci da kuma irin wurin da aka same shi, amma ina ganin bazai sami wata matsala ba".

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG