Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Magidanta Sun Koka Da Rashin Kudi A Bikin Sallah


Magidanta da dama sun koka dangane da halin rashi sakamakon halin da kasar ta shiga na tabarbarewar tattalin arzikin kasar, mafi akasari dai sun bayyana rashin kudade a hannunsu a matsayi wata barazana ga bukukuwan sallah yayin da aka shiga kwana na biyu ga sallah.

Mafi yawa dai na cewa wani lokacin ma da kudinka kake bukata amma sai ka tarar da dogon layi a wurin zarar kudi a na'urorin ATM sakamakon cikowar jama’a.

Inda wasu ke cewa sallah ta zo musu da tsammatsi na rashin wadata domin iya gudanar da bukukuwan sallah a jiya lahadi kamar yadda aka saba.

Yawanci matasa sun ce sun gudanar da salla kamar yadda tazo masu da kuma yiwa Allah ta’ala godiya na kasancewa cikin wadanda akayi sallah Eid fitr dasu domin a cewar wasu daga cikinsu akwai da damar da aka fara Azumin dasu amma ba a kare da su ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:33 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG