Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Duniyar Fina Finai Tare Da Jaruma Rahama Sadau


Jaruma Rahama Sadau
Jaruma Rahama Sadau

Shirin duniyar fina finai na wannan makon ya sami bakoncin sabuwar Jaruma a masan’antar fim ta Kannywood wato Rahama Sadau wacce tace rawa na daga cikin abin da ya ja hankalin ta harkar fim.

Rahama dai ta fara harkar fim a shekara ta 2013 kimanin shekaru biyu kenan, ta dai fara sha’awar yin wasan kwaikwayo irin na cinema da rawa tun tana makarantar sakandare. Tun dai da ta fara yin wannan sana’a tana mai da hankali akan duk yanayin da ta sami kanta.

Ta bayyana wa wakiliyar Dandalin VOA Baraka Bashir yadda take jin dadin duk fina finan da tayi a baya, hakan ya faru ne a dalilin tace duk wani shiri da aka kawo mata ta kuma tabbatar baiyi mata ba. Rahama ta godewa Allah ga yadda take yin fim taji tana sansa amma da zarar tayi wani sabon fim to zata ji tafi son sabon.

Jaruma Rahama ta nuna soyayyarta ga duk jama’a da yadda ake nuna mata so da kauna, domin dalilin mutane ta yi suna inda tace wani lokaci har kuka take in ta ga soyayyar da mutane suke nuna mata. Burin Rahama dai shine ta zama babbar Jaruma a duniya ta yadda zata zama abin koyi ga na baya.

XS
SM
MD
LG